Wane Irin Abinci Ya Kamata Ka Ci Idan Kana Da Ciwon Olsa, Gymbon Ciki?

Yanke shawarar abin da za ku ci yana da wahala sosai.

Yi tunanin yadda yake zama wahala idan kuna da ciwon gyambon ciki ‘Olsa’ wanda zai hana ku cin abincin da kuke so.

Ga wadanda daga cikinku suke da ciwon olsa, zabar abincin da zasu ci na iya zama da wahala.

Don haka mun yi bincike kuma a ƙasa akwai wasu abinci waɗanda za su taimaka wajen kariya da gyaran ƙoƙon ciki, wato gyambon ciki ko olsa da aka fi sani.

1. Zuma: An san amfanin magani na zuma shekaru da yawa. Bincike ya nuna cewa zuma ba wai kawai yana da amfani ga santsin fata da warkar da raunuka ba, amma ana ganin tasirin zuma ga gyambon ciki.

Zuma na da amfani wajen kawar da ciwon olsa. Za’a iya shan zuma cokali daya kowace safiya ko kuma a saka a safe.

2. Madarar Yoghurt: Wani muhimmin abin karin kumallo ko abincin tsakiyar rana, masana sun kuma bayyana cewa, wannan madarar mai gina jiki tana da “kyakkyawan sinadaran yaƙi da ƙwayoyin cuta” waɗanda ke taimakawa rage kumburi, hana kamuwa da ƙwayoyin cuta a cikin ciki, inganta lafiyar tumbi, da ƙara samar da ƙwayoyin rigakafi kwayoyin cuta.

Sun ce Yoghurt babban tushen calcium, bitamin D, furotin, da potassium ne.

3. Tafarnuwa: An amince da ita don maganin kashe kwayoyin cuta, maganin fungal, tafarnuwa ana ba da shawarar sau da yawa don magance mura da sauran cututtukan ƙwayoyin cuta.

To, idan ba ku sani ba, shi ma babban abinci ne don magance ciwon ciki domin yana lalata kwayoyin cutar da ke haifar da su.

Ɗauki capsule na tafarnuwa sau biyu a rana ko ƙara tafarnuwa a dafaffen abinci.