Kasuwanci
Binance Ya Rufe Sashen P2P A Najeriya
A yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa don ceton Nairar da ta lalace, babbar manhajar hada-hadar kudin Crypto ta duniya, Binance, ta rufe ayyukan ta na tsara-da-tsara na cinikayya (P2P) ga masu amfani da shi daga Najeriya.
Ayyukan tsara-da-tsara, wanda aka fi sani da P2P, yana bawa masu amfani, masu siye da masu siyarwa damar kasuwanci ba tare da tsangwama na ɓangaren wata doka ba.
P2P yana baiwa masu amfani da Najeriya damar yin ciniki crypto da dala lokacin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya haramta cryptocurrency a shekarar 2021.