Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Na Binciken Basussukan Nasir El-Rufa’i

A ranar Talata ne Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fara binciken wasu basussuka a kasashen waje da na cikin gida da gwamnatin da ta shude ta Mallam Nasir El-Rufai ta karba.

Majalisar ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da binciken a zauren taron na ranar Talata wanda shugaban majalisar, Yusuf Liman Dahiru ya jagoranta.

An ba wa kwamitin alhakin fara “binciken gaskiyar ma’amalar kudi, lamuni da tallafi da sauran ayyukan aiwatarwa daga 2015-2023”.

Kwamitin binciken ya bada umarnin gayyato El-Rufai da wasu manyan mutane ciki har da tsohon shugaban majalisar wakilai ta 8 da ta 9.

Sauran wadanda za a gayyata sun hada da tsoffin kwamishinonin kudi da kuma tsoffin kwamishinonin kasafin kudi da tsare-tsare.

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya koka da dimbin bashin da gwamnatin da ta shude ta bari wanda ya yi ikirarin gazawa gwamnatin sa.