Wasanni

Dalilin Da Yasa Nike Zaune Tare Da Mahaifiya Ta – Ronaldo

Wani dan jarida ya taba tambayar Cristiano Ronaldo dalilin da yasa har yanzu mahaifiyarsa ke zaune tare da shi kuma me yasa bai gina mata gida ba.

Ronaldo ya mayar da martani da cewa mahaifiyarsa ta rene shi kuma ta sadaukar da rayuwarta gare shi. Zata kwanta da yunwa domin shi yaci abinci.

Bamu da kuɗi, kuma ta yi aikin kuyanga kwana 7 a mako da dare don kawai ta saya masa takalmansa na farko don ya cim ma burinsa na zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa.

Ronaldo ya yabawa mahaifiyarsa duk nasarorin da ya samu kuma ya ce muddin tana raye za ta kasance a gefensa.

Tana da duk abin da zan iya ba ta kuma ita ce mafakar ta ce, kuma babbar kyauta ce gare ni. Inji Ronaldo.