Nishaɗi

Jarumar KannyWood, Saratu Gidado, Daso Ta Rasu

Daga Allah muke, kuma mu masu komawa ne a gare Shi dukkan mu.

Mun samu labarin rasuwar jarumar fina-finan Hausa, KannyWood, Saratu Giɗaɗo, kamar yadda muka samu rahoton, ta rasu ne kwanciya barci bayan kammala Sahur a yau Talata.

Haka zalika, an yiwa jarumar sallar jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada da misalin karfe 4 zuwa 5 na yamma.