Amfanin Kyankyaso Wajen Karawa Mutane Lafiya

Masana harkokin sun gano amfanin cin naman Kyankyaso da kuma shan nonon Kyankyaso wanda mutane da dama ba su san amfanin shi ba.

Masanan sun bayyana cewa, ruwan dake jikin Kyankyaso yafi nonon Shanu amfani, domin yana dauke da sinadaran gina jiki da dama wanda suka hada da ‘suga’ da kuma sinadarin ‘fat’ mai sa ƙiba da kuma ‘furotin’ mai gina jiki da kara lafiya kamar yadda wani bincike na gidan talabijin na CNN ya bayyana.

Banda ma amfanin ruwan na Kyankyaso, shi kan shi Kyankyason na da matukar zaƙi sannan kuma ga amfani ga lafiyar jikin dan adam, domin dadin naman Kyankyaso kamar abin kwalama irin ‘Ice cream’ ne, in ji masu binciken kan amfanin Kyankyaso.

“Ruwan Kyankyaso dai yana gina jiki matuka sosai” Inji wani masani Leonard Chavas da yayi bincike a kan Kyankyaso.

Yace “Nonon matar Kyankyaso har ta kai ma yafi nonon Shanu kara karfi da kara lafiya a jikin dan Adam kwarai da gaske.

A sauran kasashe dai kamar irin su China ana kokarin ganin yadda za a rika gyara ruwan Kyankyaso domin a maida shi abin kalaci na yau da kullum ga al’ummar kasar domin haɓaka lafiyar su.