Nishaɗi

An Haramta Fina-Finan Fadan Yan Daba Da Harkar Yan Daudu A Kano

Biyo bayan korafe-korafen da al’umma keyi a kan shirya fina-finan dake nuna fadan yan daba da harkar yan daudu a jihar Kano. Shugaban Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar, Abba El-mustapha ya bada umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan dake nuna fadan yan daba da harkar yan daudu a fadin Kano.

El-mustapha ya bada wannan umarni ne a yau jim kadan bayan wata ganawa da yayi da manyan ma’aikatan hukumar tace fina-finai tare da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta KannyWood wadanda suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS DIRECTORS da kuma PRODUCERS.

El-mustapha ya kara da cewa doka ce ta bawa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin yaci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar dake jihar, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za’a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su cigaba da yaduwa a cikin al’umma.

El-mustapha ya godewa yan masana’antar shirya fina-finan ta KannyWood dangane da hadin kai da kuma goyan bayan da suke bawa hukumar a koda yaushe.

A karshe ya kara godewa al’ummar jihar Kano kan irin hadin kan da suke bawa hukumar musamman na sanar da ita duk wani abu da suke ganin ya saba da al’ada tare da tarbiyar addinin musulunci.

El-mustapha ya kuma yi alkawarin ci gaba da barin kofar sa a bude domin karbar shawarwari ga duk wadaanda suke da bukatar hakan.

Sanarwa daga:
Abdullahi Sani Sulaiman
jami’in yada labarai na Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano.

Advertisement