Labaran Crypto: Muhimmiyar Sanarwa Game Da ‘AVIVE’ Coin

Idan masoya harkar kuɗin dijital, Crypto basu manta ba, a watan January da February na wannan shekara, 2024, Avive link suka bayar inda suka ce kowane mutum yaje yayi mallaki coin ɗin shi da yayi mining kuma suka sakar masa, wanda shi kuma claiming za’a buƙaci gas fee domin fito da coin, da yawan mutanen da suka yi mining basu yi claiming na coins din su ba, inda kuma wasu Wallet address ɗin da suka bayar na (OKX Exchange) ne bana kantagairar wallet ne ba. Anan ne Avive suka ce wannan watan na March da ya mutu kowa za’a tura masa a coins din shi wallet ɗinsa ba claiming za’a yi ba, haka zalika, Avive ne zasu ɗauki nauyin duka fee ɗin da za’a biya wajen tura wa ko coins din shi.

Amma kuma, kuskuren da wasu mutane suka yi na saka Wallet address na Exchange, (OKX) bayan kuma sun saka UID na OKX din, saboda da haka ake bukatar su cire Wallet address ɗin nan su saka na Wallet (Metamask ko Trust Wallet) saboda nan gaba in sun ce claiming za’a yi ba zasu biya fee ba, kowa yana da damar da zai yi claiming bayan yayi connecting wallet ɗinsa, sanin kowa ne Exchange ba’a claiming da ita.

Bugu da kari, Avive sun dakatar da mining, amma kamar yadda ya faru da ICE, sunce za’a rika shiga ana yin clicking, kamar dai mining da muke yi, amma kuma shi ba za’a baka coin ba, kawai tabbatar kana biye da sune, kuma idan mutun yayi kwana uku bai yi ba, zasu kwashe 0.1% daga coins ɗin shi.

Duk waɗanda suka cika dukkan sharuɗan da aka zayyana, zasu ci gaba da amsar ɓangare na Coins ɗin su a kowane wata, duk wanda kuma bai yi claiming ba, Coins ɗin shi za’a shigar dashi ‘bital-mali’, ko kuma in team yaga dama bayan wata shita, zai biya maka fee ya tura maka coin ɗin ka na wata shida a dunƙule a Wallet ɗinka, amma wannan zabin su ne.

Zancen Karshe

Wannan sune abin da Avive suka fitar, sai dai basu faɗaɗa bayani akan waɗanda suke da matsalar score ba, da kuma wadanda basu taɓa amsar coin ko sau ɗaya ba, ina fatar zasu yi haka a update ɗin su na gaba, ko kuma su sauya ra’ayin su bayan anyi check-in suce zasu sakar mana haƙƙin mu gaba ɗaya, Insha Allah.