INEC Ta Gargadi Jam’iyyun Gabanin Zaben Gwamnan Ondo

Yayin da zaben gwamnan jihar Ondo ke kara karatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da wani sako mai karfi ga jam’iyyun siyasa.

Kwamishiniyar zabe ta jihar Ondo, Misis Oluwatoyin Babalola, ta bukaci dukkan jam’iyyun da su bada fifiko ga bin dokokin zabe a lokacin zaben fidda gwanin da zasu yi.

Kiran ya zo ne a wata ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa a Akure, babban birnin jihar a ranar Juma’a. Jimillar jam’iyyu 19 ne suka nuna sha’awar shiga takarar gwamna, wanda aka shirya yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024. A watan Afrilu ne za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun.

Misis Babalola ta jaddada muhimmiyar rawar da jam’iyyun siyasa ke takawa wajen ganin an gudanar da sahihin zabe da gaskiya. Ta jaddada mahimmancin jam’iyyun su bi tsarin mulkin su na cikin gida, dokoki, da ka’idoji tare da kafa dokokin zabe yayin gudanar da zaben fidda gwani.

REC ta ce, “Hukumar ta samu sanarwa daga jam’iyyun siyasa kan yadda za a gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamna da aka sanya a gaba daga ranar 6 zuwa 27 ga Afrilu.

“Taron wata dama ce ta tattaunawa da jam’iyyun siyasa kan zabukan fitar da gwani na jam’iyya mai zuwa wanda ke wakiltar wani muhimmin lokaci a tafiyar dimokuradiyya a jihar. Anf rawar da jam’iyyun siyasa ke takawa wajen tabbatar da samun nasara da daidaiton tsarin ba za a iya wuce gona da iri ba”, in ji ta.

Sakon na INEC na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar yiwuwar samun kurakurai a lokacin zaben fidda gwani. Ta hanyar bin hanyoyin da suka dace, jam’iyyun za su iya taimakawa wajen tabbatar da an samu sauyi cikin babban zabe da tabbatar da amincewar jama’a kan tsarin dimokuradiyya.