Sheikh Daurawa Ya Ajiye Shugabancin Hisbah Bisa Fitsarar Yan Fina-Finai
Sheikh Aminu Daurawa Yayi murabus daga mukamin babban kwamandan Hisbah a Kano bisa dalilai da suka shafi yadda yan finai-finai da sauransu ke lalata tarbiyyar yara kuma suke samun goyon wasu mutane.
Malamin ya bayyana haka ne awani sakon video na tsawon mintuna uku. Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwa game da salon da hukumar Hisbah ke gudanar da ayyukan ta.
Idan za’a iya tunawa, Gwamna Abba Yusuf ya soki yadda yan Hisbah a wani lokaci ke dukan fitsararrun mutanen da suke kamawa, musamman yan TikTok masu yada alfasha da kuma maɗigo.
A karshe Sheik Daurawa ya yiwa Gwamnan Kano fatan alkairi bayan ya sanar da ajiye mukamin yana mai nuni da cewa ba zai iya aiki a wannan yanayin ba da wasu ke lalata tarbiyyar yayan musulmai, sannan kuma babu wani mataki da ake dauka akan su, sai dai wani lokaci idan an kama su daga baya sai a sake su.
Tun ba yau ba, Sheikh Daurawa ya sha nanata irin wannan matsalar ta idan sun kama masu laifin sun kai ofishin yan sanda ko kotu sai a sake su daga baya su koma su ci gaba da aikata fitsarar su.
Duk a kan wannan batun, a kwanakin nan aka saki wata fitsarrariyar yar TikTok Murja Kunya bayan da Hisbah ta tsare ta bisa laifukan yaɗa alfasha a yanar gizo, TikTok, Youtube, da Facebook da ka iya lalata rayuwar yara a addinance.