Kasuwanci
Farashin Giya Zai Tashi A Najeriya Karo Na Uku A Shekara Daya
Farashin giya a Najeriya na shirin tashi a karo na uku cikin kasa da shekara kamar masu hada kayan suka sanar saboda dalilai daban-daban.
A cewar Kamfanin Breweries na Najeriya masu samar da kayan shaye-shaye, wanda ya fi dadewa kuma mafi girma a kasar, duk wannan karin kudin ya faru ne bisa ga tsadar kayan goba da kuma faduwar darajar Naira.
Darajar Naira ta yi kasa sosai akan kudin kasashen waje, inda ake canja dalar Amurka $1 akan Naira N1,598 ko fiye.