Kasuwanci

Binance Ya Ce An Rufe Shafin Yanar Gizon Shi A Najeriya

Babban dandalin ciniki na cryptocurrency na duniya, Binance ya tabbatar da toshe gidan yanar gizon shi da sauran dandamali na cryptocurrency ga masu amfani da shi daga Najeriya.

Dandalin ciniki na cryptocurrency ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis yayin da ‘yan Najeriya ke korafin gaza shiga gidan yanar gizon dandalin Binance.

“Muna sane da cewa wasu masu amfani Binance suna fuskantar matsalolin samun damar shiga binance.com, tare da sauran dandamali a cikin masana’antar,” in ji Binance.