Davido Ya Mayar Da Martani Kan Zargin Kama Shi A Kenya Bisa Safarar Kwayoyi

Fitaccen mawakin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da suna Davido, ya musanta ikirarin da aka yi na cewa an kama shi a Kenya kwanan nan.

Kamar yadda Ripples Nigeria ta habarto, wani rahoto da ke nuna cewa an kama Davido a hannun ‘yan sanda a filin jirgin saman Jomo Kenyatta na Nairobi ya yadu a ranar 1 ga Afrilu.

Rahoton da ya bayyana a kafafen yada labarai na kasar Kenya, ya ce mawaki da kuma wasu mukarraban sa guda bakwai an tsare su ne a lokacin da aka gano wasu kwayoyi a cikin jirgin masu zaman kansu da suka shiga kasar.

Sai dai a yanzu Davido ya karyata rahoton a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana cewa ba a kama shi da wani laifi ba a wani yanki na duniya ba.

Ya kuma yi amfani da kafar ya sanar da cewa lauyan sa na yin wani yunkuri na fara shari’a a kan masu yada da rahoton, wanda ya bayyana a matsayin rashin gaskiya.