Siyasa

Shugaban Kasar Senegal, Bassirou Faye Ya Nada Ousmane Sonko Firaminista

Kamar yadda aka yi hasashe, sabon shugaban Senegal da aka rantsar, Bassirou Diomaye Faye, ya nada amininsa, shugaba kuma mai ba shi shawara, Ousmane Sonko, a matsayin Firaministan kasar.

A matsayinsa na Firayim Minista, Ousmane Sonko yana da alhakin nada mambobin majalisar ministocin kasar tare da tuntubar shugaba Bassirou Faye.

Wadannan samarin sun kasance masu karbar haraji ne shekaru 10 da suka wuce, tare da wasu matasa suka taru domin kafa wata kafa ko jam’iyya mai suna PASTEF, a shekarar 2014 karkashin jagorancin Sonko. Yanzu suna da alhakin tafiyar da kasar shekaru 10 kacal bayan wancan kokari.