Tarihin Jarumin NollyWood, Adam A Zango

Adam Abdullahi Zango wanda aka fi sani da Usher, Gwaska ko Adam Zango, mawakin Hausa ne, jarumi, darakta. An haife shi a gidan Malam Abdullahi da Hajiya Yelwa Abdullahi a karamar hukumar Zango ta Jihar Kaduna, Najeriya, a ranar 1 ga Oktoba 1985.

Adam A Zango bai kammala jami’a ko polytechnic ba. Ya yi imanin cewa ilimi ya ƙunshi fiye da samun difloma ko satifiket kawai. A tsakanin 1989 zuwa 1996 ya yi makarantar firamare, daga 1996 zuwa 2001 ya yi makarantar sakandare. Ya fara fitowa a fim din Hausa mai suna ‘Surfani,’ amma fina-finan Kallabi da ‘Zabari’ da ‘Raga’ da ‘Kawanya’ ne suka sa shi ya shahara.

Adamu Zango yana kallon Ali Nuhu Mohammed a matsayin jagora kuma malami. Ya yi ikirarin cewa Ali Nuhu ya koya masa yadda ake wasan soyayya. Akwai lokutan da Ali Nuhu ya zaunar da shi ya yi masa nasiha kan yadda zai rika nuna hali a cikin rawar soyayya, kamar yadda jarumin ya bayyana.

Shi ma Adam zango mai taimakon al’umma ne kuma ya yi tasiri a rayuwar mutane da dama musamman matasa. Daya daga cikin tasirinsa shine Adam Zango ya biya Naira miliyan 47 a watan Oktoban 2019 don taimaka wa yara da marayu su ci gaba da karatun su.

Ya kasance abin koyi ga yawancin matasa a Najeriya kuma ya zaburar da mutane da yawa don cimma burinsu.