Shawara Ga Maza Masu Shan Magungunan Kara Kuzarin Jima’i

Babu bukatar shan wasu magungunan ƙara kuzarin jima’i da basu dace ba domin kawai sanya ka dade baba yi inzali ba ne wanda, a ma’anar titi, yana nufin “A DADE SOSAI”.

Amma yayin da ka daɗe kana jima’i, kana ƙara matsa lamba ne akan zuciyar ka.

Ko a lokacin saduwar al’ada, bugun zuciyar ka yana ƙaruwa tsakanin kashi 40 zuwa 50 cikin 100 idan ka kusa inzali.

Shin ka tambayi dalilin da yasa yawancin maza suke barci bayan jima’i?

Yanzu, idan ka sha magungunan haɓaka jima’i, ya kai matakin da za ka ji cewa ka wadatu kuma abin da kake so shine fitar da maniyyi.

Amma ina, ba zai zo ba.

Don tilasta shi fitowa, dole ne ka sami zuciya, domin taka ta rika ta gaji.

A lokacin idan ZUCIYA bata da karfi mutumin Allah ya jikan ka, domin zai kira ka kiyama.

Kuma bayan dan lokaci, mun fara shirya jana’izar ka.

Kuma wallahi, idan sun dafa abinci, zamu ci, domin ba zamu yi kuka ba.

Bari ta kira ka “NAMIJIN MINTI BIYU”.

Kada ka ji babu dadi.

Idan kun yi AWA UKU kuna jima’i, ku da abokin zaman ku ne kaɗai kuka sani ko kuma duk wanda ɗayan ku ya faɗa wa.

Jami’i ba gasa ce ba za’a faranta muku rai kuma zaku karɓi LAMBAR YABO ba.

Bayan haka, idan ka kasance sama da shekara 50-55, kada kula yi ƙoƙarin burge kowace mace ta hanyar jima’i.

Ko Matar Ka!

Idan ka mutu, wani mutum zai karbi ‘FILIN WASAN’!

Wato idan wannan ‘filin wasa’ ba a ma kai wa wani shi ba lokacin da kake da rai ba.

Kamar dai yadda kungiyar kwallon kafa ta Inter da AC Milan ke amfani da filin wasa ɗaya San Siro!

Maza, kalma ta isa.