Kimiyya

Abinda Ya kamata Ka Sani Kan Kasuwancin Crypto Domin Cin Riba

Wani abu da ya kamata ka sani wanda zai taimaka a kasuwancin Crypto shi ne: Coin ɗin da yake kan tashi, kuma mutane suke ta magana akan shi, kada taba tunanin saka masa fiye da dala $10 ba a wannan lokacin.

Saboda idan dai ban sayi Crypto ba lokacin da babu wanda ke magana akan shi ba, gaskiya baka kyautawa kan ba idan har sai ka jira lokacin da yake yake kan ganiyar tashi sannan zaka siya.

Ya kamata ka sani cewa kasuwar Crypto tana da coins sun fi dubu 50K, don me zai sa ka riƙe soyayyar wani coin guda ɗaya bayan baka siye shi ba sanda yake ƙasa warwas ba?

A karshe, abinda ya dace shi ne ka siya a lokacin da l babu wani mai zancen coin din, idan har ka yarda da kanka, kuma kake tunani da yanke shawara a madadin ka, ba wai kabi ruguguwar soshiyal midiya ba.

Duk lokacin ka yi imani da kanka cewa zaka iya, to hakika lalle zaka iya, kuma kayi nasara.