Maganin Da Ake Yi Da Jakuna Ya Sanya Sata Da Yanka Jakuna Suka Yawaita
A kasar Sin, wato China, Ejiao magani ne na gargajiya da ake amfani da shi don cututtuka daban-daban. Ana iya narkar da adadin gram 5 zuwa 10 a cikin ruwan zafi ko ruwan inabi sannan a hada shi da sauran sinadaran da ke cikin magungunan gargajiya na kasar Sin ko kuma a sha shi kadai domin sha a matsayin magani.
An yi imanin cewa wani sinadarin gelatin dake cikin fatar jaki yana magance yanayi iri-iri kamar zubar jini, tashin hankali, rashin barci da bushewar makogaro, mura da tari, duk da rashin shaidar likatanci akan hakan. Duk da haka an gano cewa yana da tasirin hematopoietic, yana ƙara yawan samar da kwayoyin jini a cikin jikin dan Adam.
Yawancin masana’antun dake samar da maganin na mai suna Ejiao, ko mai suna “gu yuan gao” da yaren China a lardin Shandong. Gu yuan gao an yi shi ne da Ejiao, goro, sesame, dabino na kasar Sin da girkin giya. Haka nan za’a iya amfani da shi azaman suturar dabino, yana samar da wani nau’in abun ciye-ciye.
A tsakiyar shekarun 2010, farashin jakuna a wurare da yawa a duniya ya fara tashi sosai saboda yawan buƙatar Ejiao. Uganda, Tanzania, Botswana, Niger, Burkina Faso, Mali, da Senegal sun hana fitar da jakuna zuwa China.
A watan Nuwambar 2017, PETA Asia ta fitar da faifan gani da ido da ke nuna jakunan da ke fama da rashin kyau da kuma kulawa a gonaki. A watan Nuwambar 2019, Gidan Jaki ya ba da rahoton cewa ana buƙatar fatun jakuna miliyan 4.8 don biyan bukatun duniya na samar da maganin, Ejiao, dalilin da ke haifar da raguwar yawan jakuna a duniya.
Bukatar fatun jakuna na da nasaba da raguwar yawan jakuna a arewa maso gabashin Brazil, lamarin da yasa kotun tarayya ta Brazil ta dakatar da yankan jakunan da ake fitarwa zuwa China.