Al'umma
Gaskiya 8 Masu Wahala Game Da Rayuwa
- Idan kana da kyakkyawar niyya, ba za ka rasa mutane ba. Sune zasu rasa ka.
- A zamanin yau, batun shi ne, mutane ba sa daraja mutanen kirki. Maimakon haka, suna ƙoƙari su yi amfani da su.
- Waɗanda ba za su iya gane shirun ka ba, ba za su taɓa fahimtar maganar ka ba.
- Kada kayi rigima da wanda baya tsoron zama shi kadai. Kullum za ka ƙare har asara.
- Ka kula da abin da ka hakura da su domin kana nunawa mutane yadda za su yi maka.
- Mutane za su lura lokacin da ka canza halin ka zuwa gare su, amma ba za su gane yadda ayyukan su ya haifar da canjin halin na ka ba.
- Idan ka fahimci yadda mutane suke saurin mantawa da marigaya, (mutanen da suka mutu), za ka daina ƙoƙarin burge wasu mutane.
- Ayyuka suna bayyana ainihin halayen mutum, yayin da kalmomi kawai ke nuna wanda yake burin kasancewa.