Al'adu
Jihar Borno Tayi Bikin Al’adu Na Kanuri Mafi Girma A Duniya
Jihar Borno dake Arewacin Najeriya ta gudanar da bikin al’adun kabilar Kanuri mafi girma a duniya a Maiduguri wanda ya janyo ‘yan Kanuri kasashen Nijar, Kamaru, Senegal, Chadi, Libya, da dai sauransu.
World Kanuri Submit tare da armashi mai tarihi wanda ya kasance shekaru 1350 ana gudanar da shi a Maiduguri yanzu.
Daukacin abokan Kanem da Kanuri sun hallara a dandalin Ramat, Dubban mutane ne suka hallara domin shaida wannan gagarumin biki.