Amfanin Jigida A Kwankwason Mata, Akasari ‘Yan Mata

Jigida sarka ce wacce mata suka fi amfani da ita musamman daga Arewacin Najeriya, duk kuwa da cewar akwai abun da mutanen da suke yiwa lakabi da Birjani, shakka babu ya danganta da yanayin al’adar mutane, amma maza ko mata suna yin amfani da ita.

Bisa ga al’adun gargajiya mutanen Afrika baya ga kwalliya, akwai wasu dalilai da yasa suke saka jigida musamman mata.

A wasu yankunan ana hada jigida mata su saka domin samun kariya daga iska ko mutanen ko aljannu.

Wata jigidan akan haɗa da surkulle ne (tsafi) domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman kananan yara.

Wasu jigidan akan haɗa su mace ta saka a kwankwaso domin samun saukin naƙuda a wajen haihuwa.

Akwai wasu masu yakinin cewa saka jigida na taimakawa wajen rage kiba musamman ga mata masu tumbi ko katon ciki.

Jigida na taimakawa wa mace wajen ƙara girman kugu wato (Hips) a turance, da kuma samun farin jini cikin mutane, musamman ga maza.

Jigida na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo sha’awa da ra’ayin namiji zuwa ga mace a takaice.

Sai dai kuma duk da wadannan dalilan wasu mutane da dama basu son jigida, saboda a ra’ayin su jigida sarka ne da ake amfani da shi domin wani (tsafi) ko wani abu da ya sabawa addini.

Wata mata da ta shahara a hada jigida, Felicia Musa ta ce tana matukar sha’awar jigida musamman idan mace ta saka shi yana (kara) idan tana tafiya.

Ta ce jigida iri-iri ne akwai wanda wasu matan ke sakawa na farin jini ko na samun kariya, amma yi hakan ba shi ne ke mai da mutum (matsafi) ba, inji Felecia Musa.

Felicia Musa ta ce saka jigida ra’ayi ne idan kana so ka saka idan ba ka so ba za ka saka ba, amma rashin son shi din ba shi ne zai ba mutum daman cusa wa mutane ra’ayin kin shi ko rashin son shi ba.