Abincin Da Zai Iya Taimakawa Wajen Rage Ciwon Gaɓoɓi

Ciwon gaɓoɓi yana ɗaya daga cikin abubuwan dake faruwa a lokacin tsufa. Ko da yake yana daya daga cikin abubuwan da suka wajaba da za su faru yayin da kuka tsufa sosai amma wasu mutane kan yi fama da wannan a lokacin suke ƙanana, ko kuma basu tsufa ba.

Wasu daga cikin mutane ba tsufa ba ne ke haifar misu da ciwon gaɓɓai ba, sai dai ta hanyar munanan halaye da muke da su da kuma wasu irin abinci da muke ci.

Amma kuma abinci na iya taka muhimmiyar rawa wajen rage radadin gabobi.

A yau zamu yi magana game da waɗannan abincin da za su iya taimakawa wajen rage ciwon gaɓɓai ko gaɓoɓi.

1. Kifi:- Galibin kifayen masu kitse sun shahara da mai wanda yana daya daga cikin muhimman sinadarai da suke da su. Omega 3 (fat acid) da ake samu a cikin kifi mai kitse na taka muhimmiyar rawa wajen samun ingantacciyar lafiya, yana kuma da rawar da zai taka wajen rage radadin gabobi.

Wannan ya faru ne saboda yana taimakawa wajen rage kumburi a cikin jiki ta yadda zai kawar da nau’ikan ciwon gabobi da yawa.

2. Kayan lambu:– Kayan lambu irin su broccoli, Kale da farin kabeji suna da ƙarfi na gina jiki. Wannan shi ne saboda suna da wadata a cikin antioxidants, bitamin da ma’adanai masu yawa waɗanda ke da tasiri mai ban sha’awa wajen inganta lafiyar jiki da kuma rage kumburi a cikin jiki.

3. Kayan yaji da ganye:- Turmeric, ginger da tafarnuwa suna daya daga cikin muhimman ganyaye da kayan yaji a kusa. Sun kuma shahara sosai saboda abubuwan da suke da amfani ga jiki.

Nazari ya nuna cewa turmeric, ginger da tafarnuwa suna taimakawa wajen rage ciwon gaɓoɓi saboda yawan adadin ma’adanai, Antioxidants da bitamin da ke rage kumburi. Wannan kuma yana taimakawa domin rage ciwon gaɓɓai.

4. Koren shayi, (Green tea):- Koren shayi na daya daga cikin abubuwan sha da ake sha a duniya. Wannan saboda tasirinsa ga lafiyarmu yana da yawa kuma har yanzu ana gudanar da bincike da yawa akansa. Wasu nazarin sunyi imanin cewa yana da tasiri mai kyau akan lafiyar jiki.