Zaku Ji Daga Gare Mu: Iran Ta Gargaɗi Amurka Da Ingila Kan Taimakawa Isra’ila

Iran ta gargadi Amurka da Birtaniya da kawayenta kan shiga yakin da take yi da Isra’ila.

Har ila yau kasar ta Musulunci ta sanya sunan rikicin da take yi da Isra’ila da sunan ‘Aikin Gaskiyar Alkawari’.

Iran ta harba daruruwan jirage marasa matuka da kuma makamai masu linzami zuwa Isra’ila a ranar Asabar.

Masana dai na fargabar cewa hakan na iya kawo yakin da aka kwashe watanni shida ana gwabzawa a zirin Gaza zuwa wani kazamin rikici a yankin.

Kasashen Isra’ila da Iran dai sun tabbatar da harba wasu jiragen da ake kyautata zaton na Iran ne masu karfin gaske da ke kira Shaheed-136.

Dakarun tsaron Isra’ila IDF sun ce an harba jiragen sama marasa matuka 100.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce bayan sa’o’i guda kuma sun harba makamai masu linzami na ballistic a kan “mukamaiman hari” a Isra’ila a matsayin wani bangare na abin da ta kira “Alkawari na Gaskiya”.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga sanarwar da gidan talabijin din kasar ya fitar cewa, “A matsayin mayar da martani ga dimbin laifuffukan da gwamnatin Sahayoniya ta aikata. Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka a wasu wurare na musamman a cikin yankunan da Isra’ila ta mamaye.”

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa, majiyoyin leken asirin Isra’ila sun yi imanin cewa harin da ake sa ran zai kai shi ne wuraren da sojojin Isra’ila suka mamaye a tuddan Golan da ke arewa mai nisa da kuma hamadar Negev a kudu mai nisa.

Wasu majiyoyin tsaron Iraqi guda biyu sun shaidawa kamfanin dillancin labaran reuters a yayin da tashar talabijin ta 12 ta Isra’ila ta ruwaito da tsakar daren jiya cewa an fara katsalandan na farko da Isra’ila ta yi kan jiragen Iran din a gabashin Siriya da Jordan.

‘Yan tawayen Houthi na Yemen, da kuma kungiyar Hizbullah ta Lebanon, sun kuma ce cikin dare sun shiga farmakin da ake kai wa Isra’ila.

An samu rahotannin da ba a tabbatar ba a cikin dare cewa an hada jiragen Amurka da Birtaniya da na Jordan domin dakile harin na Iran.

Ministan tsaron kasar Iran, Mohammad Reza Ashtiani, ya shaidawa gidan talabijin na kasar a martanin da ya mayar cewa, “duk kasar da ta ba da damar amfani da sararin samaniyarta ko kuma kasarta domin Isra’ila ta kai wa Iran hari, za ta sami martani mai karfi daga gare mu.”