Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Tsige Sarakuna 15 Kan Rashin Tsaro, Satar Filaye Da Sauransu
Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da tsige wasu sarakunan gargajiya 15 daga kan karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, bisa wasu laifuffuka da suka shafi taimakawa rashin tsaro, satar filaye da sauransu, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu sarakuna guda hudu.
Sakataren yada labarai na gwamnatin Abubakar Bawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Talata inda ya ce daga cikin sarakunan 15 da aka sauke, an kori shida ne saboda rashin bin ka’idojin da suka dace wajen nada su.
Bawa ya kara da cewa an bar wasu mutane bakwai a wurarensu yayin da hakiman karamar hukumar Sabon Birni da takwaransa na Binji aka mayar da su gundumomin Gatawa da Bunkari.
Sanarwar ta ce gwamnati ta dauki matakin ne bisa shawarwarin kwamitin da Gwamna Ahmed Aliyu ya jagoranta tun farko ya kafa shi domin duba nadin shugabannin gargajiya da sauya sunayen manyan makarantu da kuma rusa shuwagabannin hukumomin gwamnati.
A cewar sanarwar, Hakiman Tsaki da Asara za su ci gaba da rike kujerunsu. An ba da shawarar ci gaba da bincike kan wasu da suka shafi Hakiman Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi, yayin da Hakiman Sabon Birni da na Binji aka mayar da su gundumomin Gatawa da Bubkari.
“Hakiman Unguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tullawa, Illela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu da na Giyawa, an sauke su daga mukaman da aka nada daga mukaman da aka yi musu bisa laifuka daban-daban da suka hada da taimakon rashin tsaro, satar filaye, mayar da kadarorin jama’a don amfanin kansu. da sauransu.
Hakiman Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gogono, Sarkin Kudun Yar Tsakkuwa, Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Toronkawa duk an cire su ne saboda nadin su bai bi tsari ba.”
Sakataren yada labaran ya kuma bayyana cewa an bar Alhaji Aliyu Abubakar a matsayin Ciroman Sokoto, Ibrahim Dasuki Mohammed Maccido a matsayin Barayan Zaki, Abubakar Bukari Salame a matsayin Sarkin Arewan Salame, yayin da Alhaji Aminu Aliyu Balle ya kasance Sarkin Yamman Balle.
Sauran wadanda kuma suka samu mukamansu sun hada da Alhaji Mahmud Shahu Yabo a matsayin Sarkin Gabas Dandin Mahe, Alhaji Muntari Muhammad Tukur Ambarura a matsayin Sarkin Gabas Ambarura yayin da Malam Isa Aliyu Rarah ya rike Sarkin Gabas Rara.