Sojoji Sun Gano Masana’antar Biredi Ta ISWAP A Borno

Dakarun sojojin Najeriya da ke karkashin Operation Lake Sanity III na Operation Hadin Kai a ranar Lahadi, sun gano wata masana’anta da ke samar da biredi da ke karkashin ikon kungiyar IS a yankin Maisani da ke Timbuktu Triangle a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, wanda ya bayyana hakan a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, ya ce hadakar sojojin bataliya ta 199 na musamman tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa ta Civilian JTF, sun yi karo da masana’antar biredin a aikin cin galaba na maboyar ‘yan ta’addar.

Makama, wanda ya ruwaito majiyar tsaro a cikin sakonsa, ya ce sojojin sun kuma gano wasu injunan burodi na zamani wadanda suka lalata su.

Ya rubuta: “Majiyoyin sun ce an lalata masana’antar ne yayin da kayayyakin da aka kwato sun hada da Lister guda 2, injin yin burodi guda 1, da kuma kayan burodi da dama.

“Wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda galibi su ne ke da alhakin kai hare-hare, da kwanton bauna, da nakiyoyi da suka addabi hanyar Damboa, Damaturu-Maiduguri MSR (Main Supply Route), hare-hare zuwa Askira, Buratai, Buni Yadi, da kuma lalata manyan motoci.