An Bindige Tauraruwar TikTok Ta Iraki, Om Fahad Har Lahira

An bindige wata tauraruwar TikTok ta Iraki, wacce dubban daruruwan masu bibiyar intanet suka fi sani da Om Fahad har lahira, a wani harin da aka kai da daddare a kofar gidanta da ke gundumar Zayouna a gabashin Bagadaza.

Hotunan kamarar sa ido sun dauki harin a ranar Juma’a, inda suka nuna wani maharin shi kadai sanye da kaya masu duhun gaske da kuma hular kwano yana fitowa daga babur, yana tafiya zuwa wata bakar SUV sannan ya harbi Om Fahad da ke zaune a ciki.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce ta kafa wata tawaga da za ta binciki yadda lamarin ya faru.