‘Yan PDP A Bauchi Sun Yi Zanga-Zanga Kan Dakatar Da Ningi A Majalisar Dattawa

Mambobin jam’iyyar PDP a karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi sun gudanar da zanga-zangar lumana a karshen mako domin nuna rashin jin dadinsu kan dakatarwar da aka yi wa sanata Abdul Ahmed Ningi a majalisar dattawa.

Arewa Times Hausa ta rahoto cewa an dakatar da Ningi na tsawon watanni uku bayan yayi zargin cewa an yi aringizo a kasafin kudin 2024.

A yayin da suke jawabi ga manema labarai yayin zanga-zangar, matasan Bauchi a karkashin kungiyar hadin gwiwa ta Ningi PDP Youth Groups, karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar a karamar hukumar, Alhaji Dan Lamin, sun bayyana dakatarwar da aka yi wa dan majalisar a matsayin wanda “ba a bukata kuma ba a bin tsarin dimokradiyya. “.

Lamin ya ce kungiyar za ta bi diddigin lamarin har sai an gano gaskiya a kan batun na kasafin kudin da ake zargin.

Masu zanga-zangar sun bukaci majalisar dattijai da ta janye matakin da ta dauka, inda suka tabbatar da cewa Ningi bai karya wata doka ta kasa ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Kamilu Barau Ningi, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin matasan, ya bayyana kaduwarsa da dakatarwar, inda ya dauki matakin da majalisar dattawa ta dauka bai dace ba, ya kuma bukaci a gudanar da cikakken bincike kan zargin.

Haka zalika, Shugaban riko na karamar hukumar Ningi, Ibrahim Zubairu, ya yi Allah-wadai da dakatarwar, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin bin tsarin dimokradiyya da rashin adalci.

Zubairu ya kuma zargi majalisar dattijai da kin yiwa Ningi adalci.