Labarai
Wadanda Suka Kashe Jami’an Mu Sun Kashe Zaman Lafiya – FPRO
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce wadanda suka kashe ‘yan sanda shida a jihar Delta, ba za su samu zaman lafiya ba.
A cewar wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadin da ta gabata, Adejobi ya ce: “Ba laifi kadai ba ne, har da mugunta, dabbanci, da zunubi kashe ‘yan sanda ko duk wani jami’in tsaro da ke aiki tukuru don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
“Ina kallon hakan a matsayin wani abin kunya ga al’ummar mu masu kauna. Ba zai taba zama wasa iri daya kamar yadda aka saba ba.
Hedkwatar rundunar za ta yi duk mai yiwuwa don kare lafiyar jami’an NPF tare da kashe wadanda suka kashe mana mazajen mu (jami’an mu) domin sun kashe zaman lafiya.”