Sabon Farashin Kuɗin Kujerar Aikin Hajji A 2024

Kamar yadda hukumar aikin hajjin Najeriya, (NAHCON) ta sanar mutanenza su biya kudin kujerar aikin hajjin 2024 a yanzu daga yankin Arewacin Najeriya, za su biyu Naira miliyan takwas da dubu dari biyu da ‘yan kai (N8.2 million).

Haka zalika, wadanda zasu biya daga yankin Kudu zasu biya Naira miliyan takwas da dubu dari hudu da yan kai (N8.4 million).

Bugu da kari, wadanda suka biya tuntuni, a yanzu zasu yi karin Naira miliyan daya da dubu dari tara da yan kai (N1.9 million) akan naira milyan hudu da dubu dari tara da yan kan da suka biya a baya kafin wannan karin.

Madogara: NAHCON