Addini

Referral Reward A Addinin Musulunci

Abu Huraira ya rawaito wani hadisi daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: Wanda yayi kira zuwa ga wata shiriya (ma’ana har zuwa wani abu mai abu), yana da lada, kwatankwacin ladan waɗanda suka bi shi (ko suka aikata wannan shiriyar daya kira su akanta), ladan wanda ya kira su zuwa ga shiriyar ba zai rage ladan wanda ya amsa kira zuwa ga wannan shiriyar ba, ko kuma wanda ya kira shi.

Haka zalika, wanda yayi kira zuwa ga ɓata (Allah ya tsare mu), yana da zunubi, kwatankwacin zunubin waɗanda suka bishi, zunubin daya samu ba zai ragi zunubin wanɗanda suka bi shi ba akan wannan ɓata ba.

Imamu Muslim ya rawaito wannan Hadisin a littafin sa Sahihu Muslim Hadisi mai lamba ta #6980.

Idan wani ya kira ka zuwa ga wani abu na samu, wanda bai sabawa addini ba, samun ka kai da ya kira ba zai hana nasa ba, haka zalika nasa ba zai hana naka samun ba.

Misali: da ace duk wanda Zakir Naik yake kira zuwa ga addinin musulunci sun yi leƙe, suka zai samu lada idan sun musulunta, sai hakan yasa suka ƙi amsar musulunci, su da shi wa yayi asara? Amma ga waɗanda suka amsa kiran, sai aka gudu tare ake fatan a tsira tare.

Allah kasa mu wanye lafiya.