Falalar Zuwa Masallacin Juma’a Da Wuri

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Idan ranar Juma’a ta zo, a kowane ƙofar masallaci a kwai Mala’iku, suna rubuta sunayen mutane ɗaya bayan ɗaya dake zuwa a masallaci (gwargwadon lokutan da suka zo, daga wane sai wane a isowa.

Kuma haka falalar da zasu samu ta danganta da zuwan su cikin lokaci), haka zalika, idan Liman ya zauna sai su ɗage takardun su, su zo su saurari huɗuba” wanna hadisin (Muttafaƙun alaih).

Tunatarwa: Duba da wancan zancen ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ya gabata, hakan na nufin wanda duk bai zo masallaci ba har sai bayan da Liman ya hau mimbari ya fara huɗuba, to kenan bai samu shiga wannan cikin jadawalin sunayen ba, to lalle yayi hasara wannan falalar da waɗancan da suka iso masallaci a kan lokaci za su samu.