Bambancin Sallar Kiyamul Layli, Tuhajjud Da Tarawih

1- Ƙiyamul-Layli – Ita ce duk wata sallah ta Nafila da za ka yi daga shigar duhun dare har zuwa ketowar Alfijir, a cikin Ramadan ko a wajen shi.

2 -Tahajjud – Ita ce dai Ƙiyamul-Laylin, amma in sai da a ka yi bacci a ka tashi a ka yi ta, shi ne ake kiranta da Tahajjud. Kenan an yi ta ne cikin dare ko ƙarshen shi, bayan an tashi a bacci.

3- Tarawih – Ita kuma sallar dare ce (Ƙiyamul-Layli) da a ke yi cikin azumi.

Dukansu ukun abu ɗaya ne, suna ne kaɗai suke bambanta, saboda bambancin lokutan da a ke yin su.