Labarai

Miyatti Allah Tayi Zanga-Zanga A Babbar Kotun Abuja Domin A Saki Shugabanta

Mambobin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore sun mamaye babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba 13 ga watan Maris, inda suka bukaci a sako shugaban kungiyar na kasa Bello Bodejo ba tare da wani sharadi ba.

Bodejo dai yana tsare a hannun hukumar leken asiri ta DIA tun bayan da aka kama shi a ranar 23 ga watan Janairu a ofishin Miyetti Allah da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa kan kaddamar da wata kungiyar ‘yan banga Fulani.

A ranar 5 ga watan Fabrairu ne babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya shigar da karar ta neman a tsare Bodejo har sai an kammala bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin tsare Bodejo na tsawon kwanaki 15. Bayan cikar kwanaki 15, kotun ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai da ta shigar da kara a gaban kotu kan Bodejo.

A zaman da aka yi a ranar 22 ga watan Fabrairu, alkali ya baiwa FG wa’adin kwanaki bakwai da ta shigar da karar Bodejo.

Daga baya lauyan Bodejo ya gabatar da bukatar a sake shi ba tare da wani sharadi ba. A yau 13 ga watan Maris ne ake sauraran karar.

Gabanin sauraron karar, ‘yan kungiyar Miyetti Allah sun mamaye kotun dauke da tutoci masu dauke da: “Free Bello Badejo.”

Advertisement