Matasa Sun Kashe Sojojin Najeriya 16 A Jihar Delta

Mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro, Brig.-Gen. Tukur Gusau, ya ce wasu da ake zargin wasu matasa ne sun yi wa hafsoshi 16 kwanton bauna tare da kashe sojoji 16 na Amphibious Battalion na rundunar sojojin Najeriya ta 181 da ke aikin zaman lafiya a yankin Okuoma da ke karamar hukumar Bomadi a jihar Delta a ranar Alhamis.

Gusau ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Abuja, inda ya kara da cewa wadanda aka kashen sun hada da kwamandan rundunar, Manjo biyu, kaftin daya da sojoji 12.

Ya ce an yi wa sojojin kwanton bauna ne tare da kashe su a lokacin da suke amsa wani kira na gaggawa da ya biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin Okuama da Okoloba a Delta.

A cewarsa, babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, Janar Christopher Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da cafke wadanda ke da hannu a wannan danyen aikin.

Ya kuma bayyana cewa an kai rahoto ga gwamnatin jihar Delta.

“Sojoji, duk da haka, sun ci gaba da mai da hankali da kuma jajircewa kan aikinsu na wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

“Ya zuwa yanzu, an kama wasu yayin da ake daukar matakan gano musabbabin harin,” inji shi.