Tarihin Matar Dake Akan Kuɗin Najeriya N20

1925 – 1984, macen dake kan kudin Najeriya ₦20 (naira ashirin). An haife ta ne a kauyen Kwali da ke yankin Gwari a Arewacin Najeriya, inda sana’ar tukwane ta zama ruwan dare tsakanin mata.

Matar ta kware sosai har aikinta ya zama sananne a Turai, Burtaniya da Amurka. A ƙarshen 1950s da farkon 1960s, an nuna aikinta a Landan a Berkeley Galleries. Ta zama fitacciyar mai tukwane a Nijeriya, an ba ta digirin digirgir, kuma ta samu MBE a shekarar 1963 duk da ba ta yi karatun boko ba.