Gwamnatin Najeriya Ta Gayyaci Sheikh Gumi Domin Tambayoyi

Gwamnatin Najeriya ta gayyaci malamin addinin Islama Ahmad Gumi da ke da cece-kuce domin amsa tambayoyi.

An gayyaci Gumi ne domin amsa tambayoyi kan kalaman sa kan ayyukan ‘yan bindiga a kasar nan.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Litinin.

Ministan ya ce malamin addinin Musuluncin bai “fi karfin doka ba”, ya kara da cewa gwamnati ta ga ya dace ta gayyace shi domin yi masa tambayoyi.

Makonni kadan da suka gabata, Gumi ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta hada kai da shi wajen tattaunawa da ‘yan bindiga.

Gumi ya bukaci Tinubu da kada ya maimaita abin da ya bayyana a matsayin ‘kuskure’ da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, wanda ya ki tattaunawa da ‘yan fashi.

Ya kuma ce ta’addancin da ake fama da shi a Najeriya ba ‘yan Najeriya ne ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci ba, ‘yan ta’adda ne da ke sace mutane domin neman kudin fansa.