Gwamnan Kaduna Ya Gana Da Tinubu Kan Sace Daliban Kuriga

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, na ci gaba da tsara dabarun da za a bi wajen dawo da yaran makarantar Kuriga sama da 200 da aka sace.

Arewa Times Hausa ta tuna cewa ‘yan bindiga sun sace yara ‘yan makaranta sama da 200 a Kuriga a ranar 7 ga Maris, 2024.

Sai dai tun bayan sace yaran makarantar gwamnan ya gana da masu ruwa da tsaki a jihar da suka hada da shugabannin hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya.

A ranar Asabar ne gwamnan ya bayyana cewa ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu ne domin ya ba shi shawarwari masu inganci da za a bi domin murkushe ‘yan bindiga, domin ‘yan makarantar da aka sace su samu ‘yancinsu.

Gwamna Uba Sani ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa;

“Na ziyarci masoyin shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu GCFR, domin in yi masa bayani kan matsalar tsaro a jihar Kaduna, da kuma yi masa bayani kan ingantattun dabaru don dawo da ‘ya’yan makarantar Kuriga da aka sace da kuma kaskantar da masu aikata miyagun laifuka da suka yiwa al’ummar mu kawanya. ”