Labarai
Gwamna Ya Sauke Kwamishina Kan karkatar Da Kudin Ciyarwa Na Ramadan
Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya dakatar da kwamishinan kasuwanci na jihar Alhaji Aminu Kanta bisa zargin almubazzaranci da kudaden da aka ware domin yin ciyarwa a azumin watan Ramadan.
Sakataren gwamnatin jihar Malam Bala ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa DAILY POST.
Sanarwar ta ce an dakatar da kwamishinan ne bisa zargin karkatar da kudaden da aka ware domin shirin ciyarwa a jihar na karamar hukumar Babura.
A cewar sanarwar: “Dakatar ta fara aiki nan take har sai an yanke shawarar kwamitin binciken da gwamnan jihar ya kafa domin gudanar da bincike kan zargin.”
Idan dai za a iya tunawa Majalisar zartaswar jihar ta amince da fitar da Naira biliyan N2.8 don ciyarwa a azumin watan Ramadan a fadin kananan hukumomin jihar 27.