El-Rufai Ya Bar Bashin Dala Miliyan $587 Da Naira Biliyan N85 – Gwamna Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce a ranar Asabar ya gaji bashin da ya kai dala miliyan $587 da kuma Naira biliyan N85 daga hannun tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a garin Kaduna, ya ce gwamnatinsa ta kuma gaji bashin kwangilar kwangiloli 115 daga gwamnatin da ta gabata a jihar.
Sai dai ya sha alwashin tafiyar da jihar zuwa turbar ci gaba ta hanyar amfani da albarkatun da yake da ita.
Gwamnan ya kuma lissafo muhimman abubuwan da gwamnatin sho ta saka a gaba, da suka hada da tsaro, gidaje, ilimi, kiwon lafiya, da tallafawa masu kananan sana’o’i da kanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs).
Taron ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero, tsohon babban hafsan tsaron kasa, Janar Martin-Luther Agwai (mai ritaya), mambobin majalisar zartarwa ta jihar, kakakin majalisar dokokin jihar, Yusuf Liman, da sauran ‘yan majalisa.
Haka kuma a wurin taron akwai sarakunan gargajiya da malaman addini, mambobin kungiyoyin kwadago, kungiyoyin farar hula, matasa, da kungiyoyin mata.
El-Rufai ya mika wa Gwamna Sani mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Gwamnan ya ce gwamnatin shi ba ta ci bashin kobo ko daya ba a cikin watanni 9 da suka gabata duk da dimbin bashin da tsohon gwamnan ya bari.
Ya ce: “Duk da dimbin basussukan da suka kai dala miliyan $587, Naira biliyan N85, da kuma bashin kwangiloli 115 abin bakin ciki da muka gada daga gwamnatin da ta shude, muna nan muna jajircewa wajen ganin jihar Kaduna ta samu ci gaba mai dorewa.
“Mun gudanar da cikakken nazari kan halin da muke ciki kuma muna kara mayar da hankali kan hakan. Ina farin cikin sanar da ku cewa, duk da dimbin bashin da muka gada a jihar, har yau ba mu ciyo kobo ko daya ba.”