Labarai

An Maka Jarumar KannyWood, Amal Umar Kotu Bisa Zargin Bayar Da Cin Hanci

Jarumar fina-finan Kannywood Amal Umar ta gurfana a gaban kotun majistare mai lamba 24 dake unguwar Gyadi-Gyadi a cikin birnin Kano bisa zargin yunkurin ba wa jami’in tsaro cin hanci.

Ana zargin jarumar da yunkurin bada cin hancin kudi N250,000 da aka baiwa wani jami’in ‘yan sanda mai suna ASP Salisu Bujama na rundunar ‘yan sandan Najeriya, hedikwatar shiyya ta daya a jihar Kano.

A cewar mai gabatar da kara, zargin cin hancin na da nufin dakatar da binciken ‘yan sanda kan zargin karkatar da kudi da saurayin ‘yar fim din, mai suna Ramadan Inuwa ya aikata.

Labarin ya bayyana ne a lokacin da wani Alhaji Yusuf Adamu ya shigar da kara ta hannun lauyansa, H.I. Dederi, ga Mataimakin Sufeto Janar (AIG), Umar Mohd Sanda, a ranar 18 ga Agusta, 2022, inda ya bayyana yadda ake zargin Ramadan Inuwa da karkatar da wasu makudan kudade da suka kai Naira miliyan 40 a cikin kasuwancin shi na wayar salula.

Koken ya kai ga binciken ‘yan sanda, inda ya nuna cewa Inuwa ya tura Naira miliyan N13 zuwa asusun bankin jarumar Kannywood Amal Umar.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya shiyya ta daya a Kano, CSP Bashir Muhammed, daga nan ne aka gayyaci jarumar domin amsa tambayoyi, daga nan kuma aka ba ta belin ta, amma ba a bar ta ta tafi a cikin motar da ake zargin saurayinta ya saya ba.

Advertisement