An Daure Babban Dan Crypto Shekaru 25 A Gidan Yari

An yankewa tsohon hamshakin dan Crypto, Sam Bankman-Fried hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari na Amurka saboda satar dala biliyan 8 daga abokan cinikin hada-hadar cryptocurrency FTX da ya kafa. Kamar yadda Al Jazeera da BBC News suka habarta.

Alkalin kotun Amurka Lewis Kaplan ya yanke hukuncin ne a zaman kotun Manhattan a ranar Alhamis bayan ya ki amincewa da ikirarin Bankman-Fried na cewa abokan cinikin FTX ba su yi asarar kudi a zahiri ba tare da zargin shi da yin karya a lokacin da yake bada shaida.

Wani alkali ya samu Bankman-Fried, mai shekaru 32, da laifi a ranar 2 ga Nuwamba kan zamba guda bakwai da kuma hada baki da suka taso daga rugujewar FTX ta shekarar 2022 a cikin abin da masu gabatar da kara suka kira daya daga cikin manyan zamba na kudi a tarihin kasar Amurka.