Thomas Fuller: Masanin Lissafi Mafi Sauri Dan Afrika

Ranar 29 ga Disamba, 1790, ita ce ranar mutuwar shahararren masanin lissafi Thomas Fuller, wanda aka sani da “Mai lissafin tunani”.

Ya mutu a ranar 29 ga Disamba, 1790, Marigayi Thomas Fuller bawa ne dan Afirka wanda aka sani da kwarewar ilimin lissafi. An kama shi a Afirka ta hannun turawan yamma masu sahen bayi, kuma aka tura shi zuwa Amurka a cikin shekarar 1724 lokacin yana ɗan shekara 14 kawai a duniya.

Ya kware a fannin lissafi, yana iya yin lissafin da ba a misaltawa. Wata rana da suka tambaye shi dakika (second) nawa ne a cikin shekara daya da rabi, sai ya amsa tambayar a cikin mintuna biyu kacal, dakika 47304000.

Masu goyon bayan kawar da kai da farar fata sun yi amfani da basirar sa a matsayin hujjar cewa bakar fata sun yi daidai da turawa a hankali.

Thomas Fuller, babban masanin lissafi ne, amma kash an manta da tarihi.

Ranar 29 ga watan Disamba, 2024 ne yake cika shekaru 233 da rasuwa.