Alaƙa

“Ina Matukar Son Nafisa Abdullahi, Son Aure” – Inji Abu Sarki

Sunana Abu Sarki haifaffen garin Zaria, jihar Kaduna. Shekaru na 29, kuma ni mazaunin mazauni jihar Kano ne, ku taya ni isar da wannan sako dan Allah!

Sako ne kai tsaye nake son isarwa daga zuciya ta, na kamu da so da kaunar wannan Nafisa Abdullahi wato fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, KannyWood ce wacce tauraruwarta take haskawa a wannan lokaci.

Na sani cewar ba za’a taba had’a hanyar jirgi da hanyar mota ba, amma kuma ita zuciya babu ruwan ta da hangen matsayi ko daukaka,kamar yadda zuciya ta bata taba kallon Nafisa Abdullahi a matsayin da take ba wata illa, face dai kawai na san ina son ta, ina kuma kaunar ta saboda Allah. Inji Abu Sarki.

Nafisa mace ce da duk namiji za iyi mafarkin samun ta a tsawon rayuwarsa, a kowace soyayya akwai labarin bakin ciki, a kowane labarin bakin ciki karshen shi nasara ce, saboda haka ba zan taba fidda rai da abun da nake so ba duba da matsayin da kike da matsayin da nake a yanzu. Inji shi.

Na kara kasuwa sosai wallahi zuciya ta tana son ki, amma zuciya ta ita ba tada tantance matsayi ko daukaka kawai kamuwa take na yarda da hakan. Ya kara da cewa.

Dan Allah ki amincemin na ganki ko zan samu nutsuwa a cikin zuciyata Nafisa, wallahi so da kauna abu ne mai girman gaske.

Amma idan baki amince min ba, zuciya ta za ta iya samun damuwa domin na san nayi babban rashi na rashin ganin ki a zahiri da ba na yi, haka kuma zan karbi wannan bakin cikin a cikin shafukan rayuwa ta. Fata na dai ki yi rayuwar farin ciki a duk inda kike. Abu Sarki ya kammala zancen shi.

Daga: Abu Sarki