Alaƙa

Hisba Ta Yiwa Malamin Da Ya Gyara Auren Saki 3 Bulala, Ta Bulale Mata Da Mijin

Hukumar Hisba ta rashen jihar Katsina ta yiwa wasu ma’aurata bulala da suka yi komen aure bayan sun rabu saki uku, (Igiyar auren su uku ta tsinke).

Haka zalika, an habarto cewa hukumar ta kuma bulale malamin da yayi musu tafawar mayar da auren bayan saki uku sun kare.

Kamar yadda aka habarto, wannan lamarin ya faru ne a ranar Laraba a garin Ajiwa dake ƙaramar hukumar Batagarawa.

An kuma yi zargin cewa, an yiwa Yakubu Husamatu Ajiwa da Nafisa Adamu Ajiwa, (Mata da miji) buloli bayan malamin ya dawo auren.

Malamin mai suna Abdurrahaman Abdurra’uf an zarge shi da jagorancin mayar da auren akan Naira dubu hudu (N4,000).