Alaƙa

Amfanin Auren Mace Masifaffiya 7 Da Baku Sani Ba

Fa’idoji Guda 7 Na Auren Mace Masifaffiya: Daga Sheikh Aminu Daurawa

1. Zata mayar da kai mai yawan ambaton Allah.

2. Idan kana da ƙiba masifar ta kaɗai zai ramar da kai.

3. Zata sa ka dinga fita kasuwa da wuri kuma ba zaka zo gida da wuri ba, ta wannan hanyar sai tattalin arzikin ka ya yawaita, ko aikin office kake ba zaka makara ba.

4. Zata saka ka daina kallon matan mutane, sannan masifar ta zai saka kullum ka dinga goge-goge a wayar ka, kaga ka zama mai tsoron Allah.

5. Zata saka ka koma yin biyayya ga mahaifiyar ka.

6. Zata koya maka tsayuwar dare (Ƙiyamullaili) kana cewa Allah ga matata ta fitine ni, ka anan kuma ka zama mai ibada.

7. Na karshe kuma shi ne za’a dinga kankare maka zunubi saboda masifar ta.