Wurin Da Aka Yiwa Khalifan Annabi, Sayyidina Abubakar Mubaya’a

Saqifa (Larabci: سَّقِيفَة,: Saqīfah) ta dangin Banu Sa’ida yana nufin wurin da wani lamari ya faru a farkon Musulunci inda wasu daga cikin sahabban Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) suka yi mubaya’a ga Sayyiduna Abubakar a matsayin halifa na farko kuma magaji ga Manzon Allah jim kadan bayan wafatinsa a shekara ta 11 bayan hijira (632 miladiyya).

Wurin mubaya’a ga Abubakar

Saboda haka, daga cikin kayan tarihi da ajiye kuma ake adanawa a kasar Saudiyya akwai wurin da ake kyautata zaton cewa a wurin ne aka yiwa Sayyiduna Abubakar mubaya’a a matsayin shugaban musulunci bayan rasuwar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam).

Sannan kuma idan kun lura zaku ga daga gefen hannun hagu rumfar akwai wata rijiya wacce ita ce ta Sayyiduna Abubakar a kusa ga rumfar shi.

Wadannan kayan tarihi suna ajiye ne a kasar Saudiyya.

Allah ne mafi sani!