Al'umma

Ba Ni Da Niyyar Yin Aure A Rayuwar Ta – Mawaki Timaya

Shahararren mawakin Najeriya, Inetimi Timaya Odon, wanda aka fi sani da Timaya, ya bayyana a wata hira da aka yi da shi kwanan nan cewa ba shi da niyyar yin aure a rayuwar shi.

Mawakin “Cold Outside” wanda uba ne mai alfahari da ‘ya’ya hudu da wasu mata guda uku suka haifa mai, ya bayyana haka yayin da yake bayyana dalilin da yasa ba a dadewa da aure a wannan zamani idan aka kwatanta da na iyayen mu.

A cewar shi, aure a zamanin nan bai yi nasara ba domin galibin matasan da ke gaggawar yin aure ba su fahimci manufar aure ba.

Da yake jawabi, yace aure yana da kyau amma an sanya aure ya zama mara kyau saboda yawan sakin aure yayi ta karuwa a kasar.

“Yawancin mutanen da suka shiga aure ba su san cewa yana zuwa da nauyi ba kuma hakan ya haifar da mutuwa saboda ba su da cikakkiyar fahimta kafin su daura auren,” in ji shi.