Najeriya Ta Ci Najeriya: Yanda Godwin Odiye Ya Ɓarar Da Dama A Gasar Cin Kofin Duniya A 1977

A wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya tsakanin Najeriya da Tunisia a watan Nuwambar 1977, dan wasan baya na Najeriya Godwin Odiye ne ya zura kwallo a ragar Najeriya (Own goal).

Wannan lamarin, ya wargaza burin Najeriya na buga gasar cin kofin duniya a Argentina ’78, wadda ita ce ta farko a gasar cin kofin duniya.

Sai da suka jira shekaru 17 kafin daga bisani su buga gasar cin kofin duniya na farko a 1994.

Ana saura minti 15 a tashi kuma wasan ya kasance 0-0. Sai dai a kokarin da Odiye yayi na fitar da kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida Emmanuel Okala, wanda tuni ya fito ya dauke kwallon.

A wata hira, Odiye ya bayyana yadda magoya bayan Najeriya suka fusata sosai, musamman bayan da mai sharhin ya yi ihun cewa, “Najeriya ta ci Najeriya.”

Ya kuma bayyana yadda magoya bayan shi ke cin zarafi da dangin shi da kuma yadda laifin da ya shafi kwallon da ya jefa shi ya tilasta masa barin kwallon kafa.

A cewar shi, duk da cewa ya ci gasar AFCON da kungiyar Green Eagles shekaru uku bayan haka, ya san cewa “kwallon kafa ba abu ba ne.”