Mutane Haɗu Sun Mutu Wajen Turmutsitsin Rabon Zakka

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a wani turmutsutsu yayin da suke fafutukar karbar Zakka da wani dan kasuwa mai zaman kansa AYM Shafa ke rabawa a jihar Bauchi.

LEADERSHIP ta tattaro cewa turmutsitsin ya faru ne a ranar Lahadi a ofishin Shafa Holdings da ke kan titin Jos a cikin babban birnin Bauchi.

Talakawa da mabukata, wadanda a shari’ar Musulunci ake son su amfana da zakka, sun taru tun da safe suna jiran su dauki nasu zakka.

Wakilin mu ya ruwaito cewa zakka na daya daga cikin rukunan addinin Musulunci. Yana buqatar dukkan musulmi da su ba da wani kaso na dukiyoyin su don sadaka. Wajibi ne musulmi su cika wasu sharudda kafin su cancanci fitar da zakka. Adadin shine kashi 2.5% ko 1/40 na jimlar ajiyar mutum da dukiyarsa, wanda daga baya aka bayar ga mabukata da matalauta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin mu, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kimanin mutane hudu ne suka rasa rayukan su a turmutsutsun.

Ya ce wasu da dama sun jikkata, ya ce an shawo kan lamarin.