Ƙasashen Da Suka Fi Kowa Haɗuwa A Wasan Ƙarshe Ta Gasar Cin Kofin Duniya

Jamus da Argentina sune kasashen da aka fi buga wasan karshe a gasar cin kofin duniya.

Kungiyoyin biyu sun fara haduwa a wasan karshe na cin kofin duniya a shekarar 1986, Argentina ta ci 3-2.

Sun sake haduwa a wasan karshe na cin kofin duniya na 1990, Jamus ta ci 1-0.

Haka kuma a shekarar 2014, sun hadu a wasan karshe na gasar cin kofin duniya kuma Jamus ta ci 1-0 a karin lokaci.

Brazil da Italiya ita ce wasa daya tilo da aka buga fiye da sau daya a gasar cin kofin duniya.

Brazil ta doke Italiya da ci 4-1 a gasar cin kofin duniya ta shekarar 1970 sannan kuma ta doke ta da ci 3-2 a bugun fanariti a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.